Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-15 15:41:20    
Dajin duwatsu mai suna Wansheng, dajin duwatsu ne mafi dadewa a kasar Sin

cri

Dajin duwatsu mai suna Wansheng dajin duwatsu ne mafi shahara a kasar Sin, yana gundumar Shilin ta kabilar Yi mai ikon aiwatar da harkokin kanta da ke a kudu maso gabashin lardin Yunnan na kasar Sin.

Fadin shiyyar dajin duwatsun nan ya kai muraba'in kilomita 2.4. A nan ban da dajin duwatsu, kuma akwai koguna da tafkuna da ke shimfide a karkashin kasa da sauran wurare masu ni'ima. Da Malam Zhan Xudong, jami'in hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta wurin ya tabo magana a kan dajin duwatsu na Wansheng wanda ba safai a kan ga irinsa ba, sai ya bayyana cewa, "dajin duwatsu na Wansheng ya fi dogon tarihi a kasar Sin, an same shi ne yau misalin shekaru miliyan 400 zuwa miliyan 600 da suka wuce. Tsawon kogo da ke shimfide a karkashin dajin nan ya kai mita 3000. "

Malama Zhang Yan, jagorar yawon shakatawa ta ce, daga binciken da kwararru suka yi, an gano cewa, yau da shekaru miliyan 600 da suka wuce, shiyyar dajin duwatsun nan teku ne, yayin da ruwan teku ke ja da baya, rakuman ruwan teku da ruwan sama sun yi ta goge duwatsu da ke gadon teku, saboda haka duwatsun nan sun zama siffofi iri daban daban.


1  2  3