Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-15 15:41:20    
Dajin duwatsu mai suna Wansheng, dajin duwatsu ne mafi dadewa a kasar Sin

cri

In an hango dajin duwatsun nan daga nesa, za a ga duwatsu masu sigogi irin daban daban wadanda ke kaiwa da kawowa, wasu daga cikinsu sun yi kamar tsunsaye, wasu sun yi kamar damisa, wasu kuma sun yi kamar dawaki da giwa da sauran dabbobi iri-iri. Musamman ma akwai wani babban dutse wanda siffarsa ta yi kamar mafifici, tsayin mafificin dutsen nan ya kai mita 5 zuwa 7, fadinsa ya tashi mita 5 da 6, haka nan kuma kaurinsa ya kai mita 2 zuwa 3.

Bayan haka malama Zhang Yan ta kara da cewa, bayan da masu yawon shakatawa suka isa shiyyar Wansheng, kamata ya yi, su shiga bukukuwa da 'yan karamar kabila mai suna Miao ke gudanarwa. Malama Zhang Yan ta bayyana cewa, " a ran 1 ga watan Mayu na ko wace shekara, 'yan kabilar Miao su kan shirya manyan bukukuwa kamar na wasannin kokawa da shanu da kaji da dawaki ke yi don fadakar da kan masu yawon shakatawa dangane da dabi'un gargajiyar karamar kabilar Miao. Haka nan kuma 'yan wasan fasaha su kan gabatar wa masu yawon shakatawa wasannin wake-wake da raye-raye irin na kabilar Maio cikin lokaci-lokaci."


1  2  3