Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-01 18:27:31    
Ziyarar da Mr Hu Jintao ya yi a kasar Korea ta Arewa ta sami cikakiyyar nasara

cri
Lokacin ziyarar Hu Jintao a wannan gami lokaci ne da ya yi daidai na bayan samun sakamakon  wani mataki a gun shawarwari na karo na hudu a tsakanin bangarori 6 kan batun nukiliyar zirin Korea da kafin soma sabon shawarwari a tsakanin bangarori 6, saboda haka ra'ayoyin jama'a sun mai da hankali sosai ga ra'ayi da shugabannin kasashen biyu suka samu a kan batun nukiliyar zirin Korea da sabon shawarwarin tsakanin bangarori 6 . Game da wannan, Mr Wang Jiarui ya bayyana cewa, a gaskiya dai, batun nukiliyar zirin Korea da shawarwarin tsakanin bangarori 6 sun zama daya daga cikin manyan batutuwa da Mr Hu Jintao da Mr Kim Jung Il suka mai da hankali ga yin shawarwari a kai . Gaba daya ne shguabannin biyu suka bayyana cewa, an sami sakamako a gun shawarwari na karo na hudu tsakanin bangarori 6, hadadiyyar sanarwa ita ce ra'ayi daya da bangarori daban daban suka samu, saboda haka dukansu sun bayyana cewa, za su aiwatar da ita cikin hadin guiwa, babban sakatare Kim Jung Il ya bayyana cewa, bangaren Korea ta arewa zai shiga shawarwari na karo na biyar a tsakanin bangarori 6 a daidai lokacin da aka tsai da.

Lokacin da ya tabo magana kan makomar yin hadin guiwar tattalin arziki da fasahohi a tsakanin kasashen biyu, Mr Wang Jiarui ya bayyana cewa, a lokacin ziyarar, shugabannin kasashen biyu dukansu sun bayyana cewa, ya kamata a kara wasu sabbin abubuwa a cikin zumuncin gargajiya da ke tsakanin kasashen biyu a sabon karni.(Halima)


1  2  3