A ran 30 ga wannan wata, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban kasar Sin Hu Jintao ya kammala ziyarar aiki ta sada zumunta a kasar Korea ta arewa, kuma ya dawo nan birnin Beijing. A wannan rana da yamma, sashen yin cudanyar waje na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya shirya taron bayar da labarai, inda shugaban sashen yin cudanyar waje na kasar Sin Wang Jiarui wanda ya rufa wa Hu Jintao baya a gun ziyarar ya bayyana cewa, ziyarar da Hu Jintao ya yi a wannan gami a kasar Korea ta Arewa ziyara ce da aka samu nasara tare da sakamako masu yawan gaske, kuma ta cim ma burin inganta zumuncin gargajiya da ke tsakanin kasar Sin da ta Korea ta Arewa, da kuma kara wa juna amincewa da kara habaka hadin guiwar samun moriyar juna, wannan yana da ma'ana mai muhimmanci sosai ga inganta zumuncin da ke tsakanin kasashe masu abuta kuma masu makwabtaka da juna da sa kaimi ga samun zaman lafiya da bunkasuwa a shiyyar da muke zama har ma a duk duniya.
1 2 3
|