Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-01 18:27:31    
Ziyarar da Mr Hu Jintao ya yi a kasar Korea ta Arewa ta sami cikakiyyar nasara

cri
Bisa gayyatar da babban sakataren jam'iyyar aiki ta Korea ta Arewa kuma shugaban kwamitin tsaron kasa na kasar Korea ta Arewa Kim Jung Il ya yi masa ne, Mr Hu Jintao ya kai ziyara a kasar Korea ta Arewa tun daga ran 28 zuwa ran 30 ga wannan wata. Mr wang Jiarui ya bayyana cewa, Mr Hu Jintao da manyan shugabannin kasar Korea ta Arewa sun yi musanyar ra'ayoyinsu a kan huldar da ke tsakanin jam'iyyun biyu da kasashen biyu da batun nukiliyar zirin korea da sauran batutuwan da ke tsakanin kasa da kasa da na shiyya shiyya da suka jawo hankulansu duka , kuma sun sami ra'ayi daya a fannoni da yawa, ziyarar nan ta sami cikakiyyar nasara. Ya bayyana manyan sakamakon da aka samu a gun ziyarar, ya bayyana cewa, na farko, manyan shugabannin jam'iyyun biyu da kasashen biyu sun ci gaba da bayar da manufar raya huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Korea ta Arewa. Na biyu, gaba daya ne bangarorin biyu suka sake jaddada cewa, za su ci gaba da hanzarta  daidaita batun nukiliyar zirin Korea ta hanyar shawarwari. Na uku, bangarorin biyu sun karfafa cewa, za su kara sa kaimi ga yin hadin guiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashen biyu. Na hudu, bangarorin biyu sun nuna wa juna yabo sosai saboda sakamakon da suka samu wajen raya kasa.


1  2  3