Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-10-19 17:23:53    
An fara gurfanar da Saddam Hussein, tsohon shugaban kasar Iraki gaban kotu

cri

A ran 18 ga wata, Dulaimi ya gana da Saddam har cikin awa 1 da rabi. Dulaimi ya ce, ko da yake ana tuhumar Saddam cikin rashin adalci, amma duk da haka yanzu Saddam yana cike da karfin zuciya da annashuwa. A ganinsa, ba shi da laifi, kuma shi mutum ne da bai ci bai sha ba. Dulaimi ya kara da cewa, zai nemi kotun musamman da ta dakatar da tuhuma har cikin watanni uku a ranar da za a fara yin tuhumar nan, ta yadda zai kara samun lokaci mai yawa don kare Saddam daga zargin laifuffuka da ake yi masa, sa'an nan kuma za a iya gayyatar lauyoyi Larabawa da na kasashen Turai a su shiga cikin kungiyoyin lauyoyi na Saddam don kare shi daga laifuffuka.

Manazarta suna ganin cewa, ko da yake a halin yanzu, ba a san ko kotun musamman za ta amince da tambayar da lauyan Saddam ya yi don neman dakatar da saurarar shari'a har cikin watanni uku ba ko a'a, kuma ko za a fara tuhumar Saddam nan da nan ko a'a, amma duk da haka an hakake cewa, wannan tuhuma za ta zama wata babbar alama ce ga ci gaban harkokin siyasa da ake yi a kasar Iraki. (Halilu)


1  2  3