Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-10-19 17:23:53    
An fara gurfanar da Saddam Hussein, tsohon shugaban kasar Iraki gaban kotu

cri

Kotun Musamman ta kasar Iraki ta yi shiri cikin tsanaki don yin wannan tuhuma. Bisa taimakon kasar Amurka, an taba horar da alkalan kasar Iraki 5 a kasar Britaniya har cikin shekara 1 da rabi don yin tuhumar nan. Haka zalika a karkashin shugabancin kwararru masu binciken laifuffuka da masanan shari'a na kasar Amurka, kotun musamman ta kasar Iraki ta yi bincike-bincike sosai a kan zargin laifuffuka da aka yi wa Saddam, ta haka daga bisani an mayar da al'amari mai bata rai na kauyen Dujail bisa matsayin zargin laifuffuka na farko. Babban alkalin wannan kotun musamman ya bayyana cewa, ban da al'amari mai bata rai na kauyen Dujail, za a tuhumaci Saddam da sauran laifuffukan yaki 12 da laifin yin adawa da dan adam da laifin tattake hakkin dan adam.

Dangane da wannan tuhuma, a kwanakin baya, Khalil Al-Dulaimi, lauyan Saddam ya nuna a fili cewa, kotun musamman ta mika wa lauyan sanarwar yin tuhuma da takardun kai kara da abin ya shafa ne sauran kwanaki 20 da 'yan doriya kawai da soma tuhumar nan. Wannan bai dace da ajandar shari'a ba, abin da wajibi ne a yi, shi ne a mika wa lauya wadannan abubuwa kafin kwanaki a kalla 45 da soma tuhumar. Haka zalika, an kafa kotun musamman ta kasar Iraki ne a lokacin da sojojin Amurka ke yi wa kasar Iraki mamaya, ko da yake majalisar rikon kwarya ta kasar Iraki ta amince da ita a watan Agusta da ya wuce, amma dokoki da abin ya shafa ba a fara aiki da su ba. Sabo da haka kungiyar lauyoyi ta Saddam ta kalubanci matsayi da ikon kotun musamman bisa shari'a. Dulaimi ya ce, zai bayar da sanarwa a kotun cewa, kotun musamman ta saba wa tsarin mulki na kasar Iraki, ba ta da ikon yin tuhumar halalen shugaban kasar Iraki.


1  2  3