A ran 19 ga wata, an fara gurfanar da Saddam Hussein, tsohon shugaban kasar Iraki da manyan kusoshin tsohuwar gwamnatinsa da 'yan Jam'iyyar Baath ta Iraqi guda 7 a gaban kotun musamman ta kasar Iraki a wani wurin birnin Bagadaza da sojojin Amurka ke tsananin tsaronsa. A hukunce, kotun ta zargi Saddam da sauran masu laifuffuka 7 da laifinsu na yin adawa da bil-adam sabo da sun sa hannu cikin kisan kiyashi da aka yi wa mutane wadanda musulmi ne da masu ra'ayin Shi'a suka fi yawa a kauyen Dujail da ke a arewacin birnin Bagadaza a shekarar 1982, sakamakon haka mutane 143 suka rasa rayukansu. Idan wannan laifin ya tabbata a kansu, to, za a yanke wa Saddam da sauran masu laifin hukuncin kisa.
A karo na farko ne da aka yi tuhumr shugabannin tsohuwar gwamnatin kasar Iraki, tun bayan da aka tumbuke mulkin Saddam ta hanyar yaki da Amurka ta tayar a kan Iraki a shekarar 2003, haka kuma ana ganin cewa, Saddam ya shafe shekaru 23 yana rike da mulkin kasar Iraki da karfin tuwo, sabo da haka an dauki wannan tuhuma bisa matsayin irin tuhumar da ba a taba yi ba tun bayan sabon karni na 21. Wannan ya alamanta cewa, an kawo karshen zamanin Saddam, kuma ana ganin cewa, wannan zai ba da taimako ga sake tabbatar da zaman karko a kasar Iraki.
1 2 3
|