Ana iya sa lura cewa, tun bayan karshen shekarar da ta wuce, sau da yawa Koizumi Junichiro ya bayyana cewa zai yi "hukunci kamar yadda ya kamata" kan matsalar kai ziyarar ban girma a haikalin Yasukuni. Kasashen duniya suna fata zai iya sanin mutunci da tsananin matsalar nan, kuma zai yi zabe mai daidaici. Amma, abin bakin ciki shi ne, Koizumi Junichiro bai bi fatan kasashen duniya ba, ya sake kai ziyarar ban girma a haikalin Yasukuni. Wannan ba "hukuncin yadda ya kamata ba", yin hakan shi ne babban kuskure.
Abu mai muhimmanci shi ne, Koizumi Junichiro ya dakatar da kai ziyarar ban girma a haikalin Yasukuni duk da cewar jam`iyyar dake rike da mulkin kasa da sauran jam`iyyu na kasar Japan sun yi adawa sosai, kuma a cikin 'yan kwanakin da suka wuce babban kotun birnin Osaka ta kasar Japan ita ma ta yanke hukunci cewa, idan firayin ministan kasar Japan ya kai ziyarar ban girma a haikalin Yasukuni,to,wannan ya saba wa tsarin mulkin kasar Japan. Wannan ya bayyana cewa, Koizumi Junichiro ya riga ya kai matsayin mugu mai aikata abin assha kan sanin matsalar kai ziyarar ban girma a haikalin Yasukuni.
1 2 3
|