Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-10-18 15:07:35    
Danyen aikin da Koizumi Junichiro ya yi zai kawo sakamako mai tsanani

cri

A ran 17 ga wata da safe,firayin ministan kasar Japan Koizumi Junichiro ya kai ziyarar ban girma a haikalin Yasukuni inda ake tunawa da masu laifuffukan na matsayin farko a lokacin na yakin duniya na biyu. Wannan ne karo na biyar da Koizumi Junichiro ya kai ziyarar ban girma a haikalin Yasukuni daga watan Afril na shekara ta 2001 wato tun bayan da ya hau kan kujerar firayin ministan kasar Japan, wannan ne kuma danyen aikin da ya yi na bata zuciyar jama'ar kasashen Asiya da abin ya shafa da kuma keta mutuncinsu bisa biris da kiyewar da kasar Japan da sauran kasashen da ke makwabtaka da ita a Asiya suka yi. Wannan aikin da Koizumi Junichiro ke yi zai kawo mugun tasiri ga huldar dake tsakanin kasar Sin da Japan, dole ne Koizumi Junichiro ya dauki duk hakkin da ke bisa wuyansa bisa sakamako mai tsanani da ya yi bisa sanadiyar kuskuren da ya yi. Yanzu ga sharhin da wakilinmu ya bayar:

Hakikanin matsalar kai ziyarar ban girma a haikalin Yasukuni shi ne ko kasar Japan tana iya fuskantar wannan tarihi, wato sojoji na kasar Japan sun tayar da yakin kai hari. Toji Hideki, da sauran masu laifuffukan na matsayin farko na lokacin yakin duniya na biyu guda 14 da ake tunawa da su a haikalin Yasukuni dukansu su ne suka tayar da yakin kai hari da kuma masu jagoranci a cikin wannan yaki. Haikalin Yasukuni shi ne alama ta aikin kai hari ga kasashen waje. A shekarar da muke ciki, wato shekarar cika shekaru 60 da yakin yin adawa da fascist, da kuma ta jama'ar kasar Sin da suka sami nasara a cikin yakin yi adawa da harin da Japan ta yi, ya kamata gwamnatin Japan ta yi nadama sosai kan wannan yaki, don hana sake faruwar yaki kamar irin wancan. Amma, Koizumi Junichiro ya sake kai ziyarar ban girma a haikalin Yasukuni a cikin wannan lokaci, wannan ya nuna cewa, ba ya da nufin yin nadama kan yakin kai hari, kuma ba ya da nufin rokon gafara kan jama'ar kasashen Asiya wadanda suka sha wahala sosai da masu nuna karfi na kasar Japan suka yi musu, kuma ba ya da nufin fuskantar tarihin kai hari. Irin wannan gwamnati da shugaba ba su da amincewar jama'a ko kadan, yaya kasashen Asiya da dukan kasashen duniya za su iya nuna amincewa ga kasar Japan?


1  2  3