Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-10-06 17:39:50    
Indiya da Pakistan suna ci gaba da shawarwarinsu

cri
Bisa kokarin da bangarorin biyu suka yi ne, kasar Indiya da kasar Pakistan sun sami sakamako da yawa wajen gudanar da shawarwari a tsakaninsu daga duk fannoni.Musamman ma , bayan shekaru 16 da aka dakartar da taron hadadden kwamitin tattalin arziki na kasashen biyu, sai a ran 4 ga wannan wata, sun sake taron nan .

A sa'I daya kuma , ra'ayoyin jama'a sun lura da cewa, a gun shawarwarin, ministocin harkokin waje na kasashen biyu ba su sami kowane ci gaba ba wajen daidaita matsalar Kashimir wadda ta jawo hankulan bangarorin biyu sosai. Bayan shawarwarin da suka yi a ranar farko, sakataren harkokin waje na kasar Indiya Shyam Saran ya bayyana a ran 3 ga wannan wata cewa, kasar Indiya tana son daukar duk matakai kan batun kyautata halin jinkai da ake ciki tare da kasar Pakistan bisa sharadin rashin sauyawar halin da ake ciki yanzu a iyakar kasa. Game da wannan, sakataren harkokin waje na kasar Pakistan Riaz Mohammed Khan ya bayyana cewa, kasar Pakistan ta riga ta yi babban kokari ga yaki da ta'addanci da hana shigar da su daga kasashen ketare. Batun daidaita matsalar Kashimir muhimmin batu ne da za a daidaita wajen shimfida zaman lafiya da zaman karko cikin dogon lokaci a shiyyar kudancin Asiya.(Halima)


1  2  3