A ran 4 ga wanann wata a birnin Islamabad, hedkwatar kasar Pakistan, ministan harkokin waje na kasar Indiya Natwar Singh da na kasar Pakistan Khursheed Kasuri sun gama shawarwari na kwanaki biyu a tsakaninsu. A cikin sanarwar da suka bayar cikin hadin guiwa bayan shawarwarin, bangarorin biyu sun bayyana cewa, kasar Indiya da kasar Pakistan za su ci gaba da ciyar da gudanarwar shawarwari gaba daga dukkan fannoni a tsakaninsu, kuma za su yi kokarin hakika don daidaita matsalar Kashimir cikin lumana. Manazartan batun nan suna ganin cewa, kasar Indiya da kasar Pakistan suna da niyyar ci gaba da ciyar da gudanarwar shawrwari gaba daga dukkan fannoni a tsakaninsu, wannan ko shakka babu zai sa huldar da ke tsakanin kasahen biyu ta kara samun yalwatuwa.
1 2 3
|