|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2005-10-06 17:39:50
|
 |
Indiya da Pakistan suna ci gaba da shawarwarinsu
cri
Mr Singh ya soma kai ziyara a kasar Pakistan ne a ran 1 ga wannan wata bisa gayyatar da Mr Kasuri ya yi masa.A gun shawrwarin da ke tsakanin ministocin harkokin waje na kasashen biyu, gaba daya ne suka waiwayi halin da kasashen biyu suke ciki na gudanar da shawarwari na karo karo guda biyu da suka yi kafin wannan, kuma sun sami ra'ayi daya a kan halin da ake ciki dangane da gudanarwar shawarwarin . A cikin hadadiyyar sanarwar da suka bayar, bangarorin biyu sun sake jadadda cewa, ya kamata a daidaita matsalar Kashimir ta hanyar shawarwari cikin lumana, ko kadan ba a yarda da kungiyoyin 'yan ta'adda za su kafa katanga ga gudanarwar shimfida zaman lafiya a tsakanin kasashen biyu. Sanarwar ta kuma bayyana cewa, bangarorin biyu za su yi kokarin tare don samun ra'ayi daya a kan batun da ake kira "Siachen Glacier" kafin somawar karo na uku na shawarwarin da kasashen biyu za su yi a watan Janairu na shekara mai zuwa, Sa'anan kuma, bangarorin biyu kuma sun yarda da kafa cibiyar sake ganawa a tsakanin mutanen iyalan da suke rabuwa bisa sanadiyar batun Kashimir a karshen shekarar da muke ciki. bangarorin biyu sun kuma sa hannu kan wata takardar fahimtar juna a kan yin cudanyar juna sosai a tsakanin rundunonin tsaron gabobin teku na kasashen biyu da daidaita matsalar masunta da aka tsare da kuma komar da su a daidai lokaci. Dadin dadawa kuma, bangaren Indiya ya kuma gabatar wa bangaren Pakistan wata takardar fahimtar juna dangane da hana yin amfani da makaman nukiliya ba zato ba tsammani kuma ba tare da izinin da aka bayar ba.
Bangarorin biyu sun kuma shelanta bayan shawarwarin cewa, za a yi shawarwari na karo na uku a tsakanin kasar Indiya da kasar Pakistan daga watan Janairu zuwa watan Yuli, inda bangarorin biyu za su yi tattaunawa kan batun Jammu da Kashimir da batun Siachen Glacier da yaki da ta'addanci da fataucin miyagun kwayoyi da dai sauransu.
1 2 3
|
|
|