Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-10-04 17:14:47    
Jama'ar wurare daban daban na kasar Sin suna murnar ranar bikin kasa

cri
Dayake an sami hutu na tsawon kwanaki 7, shi ya sa mutane da yawa suna son je yawon shakatawa a sauran wurare. Bisa kimantawar da aka yi, an ce, yawan mutanen da suka shiga cikin jiragen kasa don yin yawon shakatawa ya kai miliyan 38, adadin nan ya fi na sauran shekarun da suka wuce yawa. Wani jami'in hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta lardin Guizhou ya bayyana cewa, wuraren da ke jawo sha'awar masu yawon shakatawa sosai su ne kauyukan da ke da halayen musamman, sa'anan kuma wasu gidajen manoma da wuraren da ke da halayen musamman na halitta a kewayen birane su ma su iya jawo sha'awar masu yawon shakatawa, wuraren da ke da wadatattun al'adun kananan kabilu su ma sun zama wuraren da ke jawo sha'awar masu yawon shakatawa a mako mafi kyau na yin yawon shakatawa.

Wurare daban daban na kasar Sin su ma sun shirya shagulgulan al'adu da yawan gaske. Alal misali a birnin Dalian, da birnin Naning da yankin musamman na Hongkong da na Macao da saruan wurare su ma sun shirya bukukuwa iri iri da yawa don murnar ranar bikin kasa.(Halima)


1  2  3