A ranakun bikin kasa, lambunan shan iska daban daban na birnin Beijing sun shriya shagulgulan murnar ranar bikin kasa, inda mutane suna kallon wasannin fasaha da aka yi, amma a kasuwanni, ana sayi kayayyaki masu inganci da masu kyaun gani iri iri da yawa.
Ranar bikin kasa rana ce da ke da ma'anar cancantar tunawa da ita, saboda haka samari da yawa suna son yin bikin aure a wannan rana. Bisa sakamakon nan ne a titunan birnin Beijing da Shanghai da Taiyuan da sauran birane, ko'ina ana iya ganin motocin da suke daukar angwaye da amare a kowace rana, wani wakilin gidan rediyo kasar Sin da ke birnin Taiyuan ya ruwaito mana labari cewa, a cikin halin da ake ciki na murnar ranar bikin kasa cikin farin ciki sosai ne, auren da aka yi a tsakanin samari maza da mata ya zama wani halin musamman mai kyau da ake ciki a birnin Taiyuan. Bisa kididdigar da wani ma'aikacin sashen yin rajistar aure ya yi, an ce, a kalla da akwai mutane 400 wato angwaye 200 tare da amarensu 200 da suka yi aure a ran 1 ga watan Oktoba. Motocin daukar wadanda ke yin aure suna wucewa tare da amon ganguna , kai, ana farin ciki da murnar ranar bikin kasa a ko'ina.
1 2 3
|