Shekarar da muke ciki, shekara ce ta cika shekaru 56 da kafa Jamhuriyar Jama'ar Sin. Daga ran 1 ga wannan wata, mutanen kasar Sin suna soma hutu na tsawon kwanaki 7. Yawancinsu suna yin bikin aure da shagalin taruwa da sauran shagulgula a lokacin hutun nan, wasu ma suna je yawon shakatawa a sauran wurare don bude idonsu, wasu ma suna yin hutu a gidajensu kawai don sakin jikinsu. A sa'I daya kuma, wasu wurare daban daban na kasar Sin suna shirya shagulgulan al'adu na samfurori daban daban da yawa don bar mutane su yi hutu sosai cikin farin ciki da jituwa.
Tun lokacin da ake shiga ranar bikin kasa, mutane suna ta kai da kawowa a filin Tian An Men na birnin Beijing a kowace rana , furanni masu kyaun gani sosai da aka dasa a nan sun jawo hankulan mutane sosai da sosai har a ce sun manta komawa gida. Tukwane fiye da dubu 300 da aka dasa furanni a ciki tare da lambunan furanni guda 4 da aka gina da ke da babban batun bayyana halayen musamman na kasar Sin sun bayyana halin da birnin Beijing ke ciki na yin matukar murna da farin ciki da jituwa don maraba da baki masu yawon shakatawa da suka zo daga ko'ina na gida da na kasashen waje. Ya zuwa daren, ana bude wuta don haskaka lambunan furanni a filin Tian An Men, kai, ana iya samun sakamakon fasaha na duba furanni da sauran abubuwa masu kyaun gani sosai da sosai .
A filin Tian Men , wani saurayi na kabilar Wa mai suna Guo Qing ya bayyana cewa, na zo nan ne daga lardin Yunnan na kasar Sin, ranar da aka haife ni tana kusanto ranar bikin kasa, shi ya sa mahaifina ya nada mini sunan Guo Qing, ma'anar sunana ita ce murnar ranar bikin kasa, saboda haka a ranakun bikin kasa na kowace shekara, tabbas ne na zo nan Tian An Men, kuma a kowace shekara, abubuwan da na ji na gani sun yi bambanci sosai, a gaskiya dai kasarmu ta sami sauyawa, kuma kasar mahaifa tana kara ingantuwa da wadatuwa.
1 2 3
|