A karkashin irin wannan hali ne,kawancen kasashen Turai ya tsai da cewa zai yi gyara kan gyararren shiri na kudurinsa.Amma a cikin sabon gyararren shirin kudurin,aka yi nuni da cewa,kasar Iran ta yi aikin saba wa `yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya`.Kazalika,a ran 22 ga wata,ministocin harkokin waje na kasashe uku wato kasar Faransa da kasar Jamus da kasar Ingila da babban wakili mai kula da harkokin waje da manufar kwanciyar hankali na kawancen kasashen Turai Javier Solana sun bayar da wani jawabi tare a kan jaridar `duniya` inda suka kirayi zaman al`ummar kasashen duniya da su gama kansu don fama da kalubalen kasar Iran.
Bangaren kasar Iran ya riga ya yi maraba ga kawancen kasashen Turai saboda ya yi gyarawa kan gyararren shirin kuduri.
Duk da haka,mun sami labari cewa,kasar Rasha ba ta gamsu da wannan ba,shi ya sa kila ne za a ci gaba da yin gyarawa kan sabon gyararren shirin kuduri,ta yadda za a sa bangarori daban daban su yarda da shi daga dukkan fannoni.(Jamila Zhou) 1 2 3
|