Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-09-23 09:59:03    
Batun nukiliya na Iran ya sami sabon ci gaba

cri

Kasar Rasha tana ganin cewa,idan aka gabatar da batun nan a gaban kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya,to,wannan zai kawo mugun tasiri ga wannan batu yayin da ake warware shi ta hanyar diplomasiya.A halin da ake ciki yanzu,muddin dai bangaren kasar Iran ya yi hadin guiwa tare da hukumar kula da makamashi ta duniya,to,tabbas ne za a daidaita dukkan matsalolin dake gabanmu.Bangaren kasar Rasha yana so ya yi kokari tare da kasashen da abin ya shafa don warware batun nukiliya na kasar Iran kamar yadda ya kamata.

A ran 22 ga wata,a gun taron kwamitin hukumar makamashi ta duniya da aka yi,zaunannen wakilin kasar Sin dake wakilci a ofishin majalisar dinkin duniya na Viena Wu Hailong ya bayyana cewa,yanzu ana yin matukar kokari don warware batun nukiliya na kasar Iran,kamata ya yi bangarorin da abin ya shafa su mai da hankali kan muhimmiyar moriyarsu ta dogon lokaci.Hukumar kula da makamashi ta duniya tana ganin cewa,ya fi kyau a warware batun nukiliya na kasar Iran ta hanyar diplomasiya kuma cikin tsare-tsaren hukumar nan,dalilin da ya sa haka shi ne domin wannan zai amfanawa zaman lafiya da zaman karko na shiyya-shiyya.Yanzu,abu mafi muhimmanci shi ne kawancen kasashen Turai da kasar Iran su maido da shawarwari tun da wur wuri.Ban da wannan kuma,kasashe `yan ba ruwanmu 14 dake cikin kwamitin hukumar makamashi ta duniya suna fatan za a warware batun cikin tsare-tsaren hukumar nan,wato ba su yarda da a gabatar da batun a gaban kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ba.


1  2  3