A ran 21 ga wata da dare,kasashe 3 wato kasar Faransa da kasar Ingila da kasar Jamus wadanda ke wakilci kawancen kasashen Turai sun yi gyara kan gyararren shiri na kudurin batun nukiliya na kasar Iran da suka gabata kuma sun tsai da kuduri cewa,ba za su nemi kwamitin hukumar kula da makamashi ta duniya da ya gabatar da batun nukiliya na kasar Iran a gaban kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ba,daga nan ana iya cewa gudanarwar yin shawarwari kan batun nukiliya na kasar Iran wadda ta shiga halin kaka-nika-yi ta sami sabon ci gaba.
A ran 20 ga wata,kawancen kasashen Turai ya mika wa taron kwamitin hukumar kula da makamashi ta duniya gyararren shiri na kudurin batun nukiliya na kasar Iran,gyararren shirin ya nemi hukumar nan da ta gabatar da batun nukiliya na kasar Iran a gaban kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya da babban taron majalisar dinkin duniya,daga baya,wato a gun taron da aka yi ran 21,kasar Amurka da kasar Japan da kasar Austrelia da kasar Canada da sauran kasashe sun yarda da wannan.Amma kasar Rasha da kasar Sin da sauran kasashe `yan ba ruwanmu da yawa sun nuna kiyayya ga wannan.
1 2 3
|