Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-09-08 20:44:31    
Ziyarar Mista Wu Bangguo ta kara zurfafa dangantaka da ke tsakanin kasar Sin da Morocco

cri
Daya daga cikin makasudin ziyarar Mista Wu Bangguo shi ne sa kaimi ga bunkasa harkokin ciniki a tsakanin Sin da Morocco. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, a galibi dai, hulda da ke tsakanin Sin da Morocco a fannin tattalin arziki da ciniki ta sami ci gaba sosai, yawan kudi da aka samu wajen yin ciniki a tsakanin kasashen biyu ya karu da saurin gaske, har ya kai dalar Amurka miliyan 1160 a shekarar bara. Haka nan kuma yayin da yake ganawa da Mista Driss Jettou, firayim ministan kasar Morocco, Mista Wu Bangguo ya bayyana cewa, yana fatan kasashen biyu za su kyautata tsarin ciniki, su kara karfin hadin guiwa a tsakanin kamfanoni da masana'antu, su hada kansu a fannin aikin su da na sadarwa da saka da kuma yin amfani da albarkatun kasa bisa ka'idojin cin nasara tare da na moriyar juna, haka zalika su kara fadada hadin guiwarsu a fannin yawon shakatawa don kai huldar tattalin arziki da ciniki da ke tsakanin Sin da Morocco zuwa wani sabon matsayi.

Ban da wadannan kuma Mista Wu Bangguo ya halarci bikin sa hannu a kan yarjejeniyar hadin guiwa tsakanin gwamnatin Sin da ta Morocco dangane da harkokin tattalin arziki da na fasaha da kuma horar da 'yan fasaha da kula da aikin saka. (Halilu)


1  2  3