Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-09-08 20:44:31    
Ziyarar Mista Wu Bangguo ta kara zurfafa dangantaka da ke tsakanin kasar Sin da Morocco

cri
A lokacin da Mista Abdrloughed Radi, shugaban majalisar wakilai ta kasar Morocco da Mista Moustapha Okachay, shugaban majalisar dattijai ta kasar suke ganawa da Mista Wu Bangguo, dukansu sun nuna babban yabo ga ma'amala da ake yi tsakanin majalisar kasar Morocco da ta kasar Sin, kuma sun bayyana cewa, majalisar Morocco tana son kara yin ma'amala a tsakaninta da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da kara karfin hadin kansu.

Shugabannin kasar Sin da ta Morocco sun sami nasarar kai wa juna ziyara a shekarar 1999 da ta 2002, kuma sun tsara manufar yalwata hulda tsakanin kasashen biyu a cikin sabon karni bisa manyan tsare-tsare da moriyarsu ta dogon lokaci. A cikin ziyarar da ya yi a wannan gami ma, Mista Wu ya bayyana wa sarki Mohammed na 6 na kasar Morocco cewa, sabuwar kungiyar shugabanninn kasar Sin tana ba da matukar muhimmanci ga yalwata dangantakar aminci da ke tsakanin Sin da Morocco, kuma tana son yin kokari tare da kasar Morocco wajen kara yin ma'amala a tsakanin kasashen biyu da kara dankon aminci a tsakanin jama'arsu da kara karfin hadin kansu don moriyar juna da kawo zaman alheri ga jama'ar kasashen biyu.

Daga wajensa, sarki Mohammed na 6 ya nuna babban yabo ga dangantakar aminci da hadin kai a tsakanin kasar Morocco da ta Sin, kuma yana ganin cewa, dangantaka da ke tsakanin kasashen biyu ta gwada wani kyakkyawan misali ga hulda da ke tsakanin kasa da kasa.


1  2  3