Ran 6 ga wata, Mista Wu Bangguo, shugaban zaunannen kwamitin majalsiar wakilan jama'ar kasar Sin ya kawo karshen ziyarar aikinsa na aminci a kasar Morocco. A lokacin ziyararsa ta kwanaki uku, Mista Wu ya yi musayar ra'ayoyi a tsakaninsa da shugabannin kasar Morocco a kan kara yin ma'amala tsakanin majalisun kasashensu biyu da yalwata dangantaka, da kara karfin hadin kai don moriyar juna a tsakaninsu da dai sauran batutuwa, kuma sun sami ra'ayi daya mai muhimmanci. Ziyarar Mista Wu Gangguo ta sami cikakkiyar nasara.
A lokacin ziyararsa, Mista Wu ya bayyana cewa, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin tana son kara yin ma'amalar aminci a tsakaninta da majalisun kasar Morocco daga fannoni daban daban, su yi musayan sakamako da suka samu wajen kafa dokoki da sa ido, don aza harsashi ga yalwata hulda da ke tsakanin kasashen biyu. Haka zalika ya kamata majalisun kasashen nan biyu su kara karfin hadin guiwarsu a cikin kungiyoyin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, don kare moriyar kasashe matasa cikin hadin guiwarsu.
1 2 3
|