Bo Xilai ya nuna yabo ga matakan da kawancen kasashen Turai ya dauka na shigar da dukkan kayayyakin saka na kasar Sin da ke jibge a tashoshin ruwa na kasashen Turai.
Wakilin ciniki na kawancen kasashen Tuirai Mandelson ya bayyana cewa, kodayake an gamu da wasu wahaloli a cikin gajeren lokaci a kan kayayyakin saka , kuma an yi mawuyacen shawarwari, amma ba a iya haifar da yakin ciniki a tsakanin kasar Sin da kawancen kasashen Turai ba, kasar Sin babbar kasa ce da ke kara samun bunkasuwa wajen yin ciniki, yi wa juna karin taimako a tsakanin bangarorin biyu wajen tattalin arziki ya tabbatar da cewa, bangarorin biyu suna da babban karfin da za su iya yin amfani da shi wajen yin hadin guiwa a tsakaninsu.
Tun daga farko har zuwa yanzu, ko ma a nan gaba, ba za a iya haifar da yakin ciniki a tsakanin kasar Sin da kawancen kasashen Turai ba, duk saboda kasar Sin da kawancen kasashen Turai suna neman biyan bukatunsu na kansu.
Mandelson ya bayyana cewa, tilas ne yarjejeniyar nan ta sami amincewar gwamnatocin kasashe 25 da ke cikin kawancen kasashen Turai .(Halima) 1 2 3
|