Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-09-07 18:19:42    
Kasar Sin da kawancen kasashen Turai sun sami ra'ayi daya a kan kayayyakin saka

cri
Bayan bikin sa hannu kan takardar, ministan kasuwanci na kasar Sin Bo Xilai da wakilin ciniki na kawancen kasashen Turai Mandelson sun gana da manema labaru na gida da na waje cikin hadin guiwa. Mr Bo Xilai ya bayyana cewa, takardar da kasar Sin da kawancen kasashen Turai suka sa hannu a kai ta bayyana halin da bangarorin biyu suke ciki na yin hadin guiwa da samun nasara gaba daya .

Game da kayayyakin saka da aka jibge a tashoshin ruwa na kasashen Turai,mun dauki matakin da kowane bangaren zai dauki nauyinsa na kansa bisa adalci sosai. Ina ganin cewa, shawarwarin da muka yi ya bayyana adalci da daidaici daga manyan ka'idoji zuwa cikakkun abubuwa.

Mr Bo Xilai ya bayyana cewa, yarjejeniyar da kasar Sin da kawancen kasashen Turai suka daddale a kan kayayyakin saka a watan Yuni na shekarar da muke ciki a birnin sxhanghai tana bisa kimiyya tare da samun nasara gaba daya, babban dalilin da ya sa aka haifar da batun jibge kayayyakin saka na kasar Sin a tashoshin ruwa na kasashen Turai, shi ne saboda bangarorin biyu ba su iya aiwatar da ajandar hukuma a cikin wata guda bisa dokokin shari'a da ka'idoji na kowanensu ba.


1  2  3