Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-09-07 18:19:42    
Kasar Sin da kawancen kasashen Turai sun sami ra'ayi daya a kan kayayyakin saka

cri

Ta hanyar shawarwarin da aka yi cikin kwanaki biyu, a ran 5 ga wannan wata a nan birnin Beijing, ministan kasuwanci na kasar Sin Bo Xilai da mamban ciniki na kawancen kasashen Turai Peter Mandelson sun sa hannu kan wata muhimiyyar takarda ,kuma sun sami ra'ayi daya wajen daidaita batun jibge kayayyakin saka da yawa na kasar Sin a tashoshin ruwa na kasashen Turai. Bisa kudurin da aka tsai da a cikin takardar , bangaren kawancen kasashen Turai zai shigar da duk kayayyakin saka na kasar Sin da yawansu ya kai miliyan 80 ko fiye da aka jibge su a tashoshin ruwa na kasashen Turai.

Don daidaita batun jibge kayayyakin saka da yawa da kasar Sin ta fitar zuwa kasashen Turai a tashoshin ruwa na kasashen Turai, daga karshen watan jiya, jami'an ciniki na kasar Sin da na kawancen kasashen Turai sun soma yin shawarwari a tsakaninsu. Bayan shawarwarin da suka yi cikin karo biyu tare da jurewar wahaloli da yawa ne, a karshe bangarorin biyu sun sami ra'ayi daya. Bisa kudurin da aka tsai da cikin takardar, kawancen kasashen Turai zai shigar da duk kayayyakin saka na kasar Sin da ke jibgewa a tashoshin ruwa na kasashen Turai. Hanyar hakika da za a bi don daidaita batun nan ita ce, za a mayar da rabin wadannan kayayyakin saka don su zama sabon karin kaso da kawancen kasashen Turai ya kara , sauran rabinsu za a rage su daga kaso na shekara mai zuwa, ko za a rage su daga kaso na sauran kayayyakin saka da za a fitar.


1  2  3