
Amma, akwai jama'ar kasar Iraqi da yawa suna ganin cewa, makasudin masu dakaru shi ne sojojin Amurka kawai, amma farar hula na kasar Iraqi su zama masu shan wahala, mamaye rashin dalilan da sojojin Amurka suka yi wa kasar Iraqi shi ne tushe na farmakin ta'adancin da aka karayi bayan yakin Iraqi. Sabo da haka, jama'ar kasar Iraqi sun bukacin sojojin kasa da kasa da ke shugabancin sojojin Amurka za su tsara shirin lokacin janye jiki, su janye jikinsu bisa halin da sojojin kasar Iraqi za su iya kiyaye kwanciyar hankali na zaman al'umma.
A sa'i daya kuma, wasu jama'ar kasar Iraqi suna nuna bakin ciki kan halin kwanciyar hankali na kasarsu nan gaba, suna ganin cewa, da kyar kasar Iraqi za ta iya maido da kwanciyar hankali da zaman karko a cikin gajeren lokaci, ko da ya ke sojojin Amurka sun janye jikinsu daga kasar Iraqi, kungiyoyi masu yin dagiya za su yi tsamani kasar Amurka za ta ci gaba da mallaka gwamnatin kasar Iraqi, kuma kwace albarkatun man fetur na kasar ta hanyar daban, hakan, ba za su daina kai farmakin yi adawa da gwamnati, yadda zai sa farar hula da yara na kasar Iraqi su ci gaba da karkashin barazanar da al'amarin fashewar boma da aka dasa a mota ke kawo musu. (Bilkisu) 1 2 3
|