Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-07-14 17:04:48    
An kara yin al'amarin fashewar wani boma da aka dasa a mota a Bagadaza

cri

Wakilinmu ya ruwaito mana labari cewa, ran 13 ga wata, daya bayan daya, sojojin kasar Amurka da ke kasar Iraqi, da bangaren 'yan sanda na kasar Iraqi suka shaida cewa, a wannan rana a shiyyar da ke kudu maso gabashin Bagadaza an yi al'amarin fashewar wani boma da aka dasa a mota a Bagadaza, wanda makasudinsa shi ne sojojin kasar Amurka, sakamakon haka mutane 27 sun rasa rayukansu, inda suka hada da yaran kasar iraqi 24, a kalla dai mutane 70 sun ji rauni. A wannan rana a wata sanarwar sojojin Amurka da ke kasar Iraqi sun bayyana cewa, akwai sojojin Amurka 1 ya mutu, yayin da 3 suka ji rauni a cikin wannan al'amari.

Wannan ne al'amarin farmakin ta'adanci na 2 da ya fi girma da ke faruwa a Bagadaza a cikin wannan mako, tun bayan da aka tayar da hare-haren kunar bakin wake a ran 10 ga wata a wata cibiyar neman sojoji da ke Bagadaza, sakamakon haka mutane 25 sun mutu, wannan kuma farmaki ne da ya sa yawan yaran da suka mutuwa ya fi yawa tun daga watan Satumba na shekarar da ta wuce. Tun bayan da aka kafa gwamnatin wucin gadi ta kasar Iraqi, akwai mutane kamar 1600 sun rasa rayukansu a miyagun aikace-aikace dabam daba, inda wasu su ne mata da yara.


1  2  3