
Bayan da aka tayar da hare-haren kunar bakin wake a ran 13 ga wata, Mr. Kofi Annan, babban sakataren M.D.D. ya bayar da wata sanarwar ta kakakinsa, inda ya nuna mamaki sosai da kuma yi zargi mai tsanani kan wannan al'amari. Sanarwar ta ce, babu dalilan da ke iya saki wa wadannan miyagun aikace-aikacen da aka yi wa farar hula, da kuma yara, kuma wadannan aikace-aikacen ta'adanci ba za su iya cimma ko wane buri. A wannan rana, Mr. Scott Mcclellan, kakakin fadar gwamnatin Amurka ya yi zargi mai tsanani kan wannan aikin ta'adanci, ya bayyana cewa, farmakin nan ya nuna cewa, masu dakarun ba su taba kula da rayukan farar hula ba, kuma ba su girmama rayukan jama'a. Ya ce, masu dakaru suna neman tauye gudanarwar dimokuradiya, amma ba su da ko wane dailai kan kisan killa farar hula, musamman yara.
1 2 3
|