
Zantawar Rumsfeld ta jawo kulawa daga wajen 'yan kasar Iraq. Wasu sun nuna cewa, kasar Amurka ta yi shawarwari da kungiyoyin dakaru na Iraq, ta yi kokari don shigad da wadannan kungiyoyi cikin ajandar siyasa, haka na anfanawa sake raya Iraq cikin kwanciyar hankali da ajandar sake shimfida halin siyasa ; in Amurka ta yi sauri wajen tsara jadawalin janye sojoji, to za a samu wani dalilin da ke sa rashin kasancewar kungiyar Al-qaeda ta Iraq da ke karkashin jagorancin Jaafari, haka zai amfanawa sake maido da kwanciyar hankali da zama mai dorewa na Iraq. Wasu 'yan Iraq sun nuna cewa, ba za a sami wadatar zuci kan sabuwar manufar Amurka ga Iraq ba, saboda an kasance da kungiyoyin dakaru masu yawa, sun damu kila shawarwarin da Amurka ta yi da kungiyoyin dakaru na Iraq zai haddasa yakekeniya tsakanin kungiyoyin dakarun Iraq wanda zai tsananta halin kwanciyar hankali da ke kasancewa yanzu. Kuma kodayake sojojin Amurka sun tanadi jadawalin janyewa daga Iraq, kungiyar al-Qaeda da sauran kungiyoyi ba za su amince da halatacciyar gwamnatin wucin gadi ta Iraq ba. Da kyar za a iya kau da harkokin kai farmaki daga wajen masu yin adawa da gwamnati. Kungiyar Al-Qaeda ta yi kashedi a ran 26 cewa, kada kungiyoyin dakaru su yi shawarwari da Amurka.(ASB) 1 2 3
|