
Ran 26 ga wata yayin da Donald H. Rumsfeld ministan tsaro na kasar Amurka ya karbi ziyarar da tashar watsa labaru na Fox ta yi masa, ya gaskanta cewa, kasar Amurka da dakarun Iraq masu yin adawa da Amurka da gwamnatin kasar sun yi shawarwari cikin sirri. Ya kuma nuna cewa, kayar da 'yan dakaru da ke cikin iyakar kasar Iraq ya zama dawainiyar 'yan Iraq, amma ba ta rundunar sojojin Amurka ba ce. Manazarta al'amura sun nuna cewa, zantawar Rumsfeld ta alamanta cewa, mai yiyuwa ne kasar Amurka za ta sauya manufarta ga kasar Iraq.
Ran 27 ga wata a Britania, yayin da firayim minista Ibrahim al-Jaafari na gwamnatin Iraq ya amsa tambayar da manema labaru suka yi masa dangane da yaya za a kalli batun Rumsfeld, ya nuna cewa, yanzu dakarun Iraq ba ma kawai na mai da mashin gaba kan sojojin Amurka da ke jibge a Iraq kawai ba, tumbuke zababben gwamnatin jama'a kuma ya zama daya daga cikin nufinsu, amma ya amince da cewa, za a tabbatar da kwanciyar hankali da zama mai dorewa cikin kasar Iraq.
1 2 3
|