
Manazartan al'amura sun nuna cewa, bayan kafuwar gwamnatin Jaafari, halin kwanciyar hankali na kasar Iraq yana kara tangadawa, aikace-aikacen sojan Amurka da ke jibge a Iraq ba su sami sakamako ba. A gaban halin nan, kasar Amurka ta ga tilas ta zauna wajen yin shawarwari da dakaru masu yin adawa da ita, don neman hanyar siyasa na daidaita batun. Bayan haka, adadin matattun sojojin Amurka na karuwa, wanda ya sa gwamnatin Bush ke fuskantar karfin matsi fiye da kima daga gida, manufarta ga kasar Iraq ba ma kawai ta gamu da kiyewa daga wajen jam'iyyar Democra ba, har ma 'yan majalisar da ke cikin jam'iyyar Republica wadda shugaba Bush ke ciki, sun kai suka sosai. 'Yan majalisar Amurka da ke kara yawa sun bukaci gwamnatin Bush da ta yi sauri wajen tsaraa jadawalin janye sojojin Amurka.
Zantawar Rumsfeld ta ran 26 ga wata ta nuna cewa, kila manufar kasar Amurka kan kasar Iraq za ta sauya. A wani fanni, kasar Amurka za ta yi kokarin kusantar kungiyoyin dakarun Iraq da warwaresu ta hanyar shawarwarin siyasa, za ta kuma banbamta kungiyar yin dagiya da kungiyar al-Qaeda ta Iraq da ke karkashin jagorancin Abu Musab al-Zarqawi, mutum na 3 na kungiyar al-qaeda, ta mai da muhimminci kan kungiyar al-Qaeda don rage karfin matsi na sojojin Amurka da ke jibge a Iraq ; a wani fanni daban kuma, kasar Amurka za ta sauya ta nuna goyon baya da horad da sojojin Iraq daga sa hannu cikin harkokin soja, taki kan taki ne Amurka ta mika wa rundunar kare kwanciyar hankalin Iraq aikin kai naushi ga kungiyoyin dakaru da kare kwanciyar hankali, ta yadda za ta fuskanci karfin matsi daga wajen kasar Amurka yayin da ta tanadi jadawalin janye sojojinta.
1 2 3
|