
Dalilan da suka sa ba a yanke wa Sadam hukunci cikin dogon lokaci ba suna kumshe da fannoni da dama,da farko dai,kotun musamman na Iraki yana so ya yanke wa manyan jami`ai na mulkin Sadam kafin za su yanke wa Sadam hukunci.Na biyu,ayyukan share fage kafin yanke hukunci sun yi yawan gaske.
Ban da wannan kuma,bangaren Sadam shi ma yana yin kokari,kungiyar lauyoyi ta Sadam wadda ke yin aiki a birnin Amman,babban birnin kasar Jordan ta kai suka ga kotun musamman na kasar Iraki saboda bai yi aiki bisa adalcia ba.Wannan ne wahala daban dake gaban kotun musamman yayin da yake yanke wa Sadam hukunci.(Jamila Zhiu) 1 2 3
|