A ran 15 ga wata,kotun musamman ta kasar Iraki ta sanar da wani faifai game da tambayar da aka yi wa`dan`uwan Sadam Sabawi Ibrahim al-Hassan da sauran manyan jami`ai na mulkin Sadam.A cikin rahoton,kotun musamman ya bayyana cewa,dalilin da ya sa suka yi aikin nan a ran 13 ga wata shi ne don yin bincike kan laifufukan da wadannan manyan jami`ai suka yi ga musulmai na rukunin Shi`a dake kudancin kasar Iraki da kurdawa dake arewacin kasar a shekarun 1980 da shekara ta 1991.
Wannan ne karo na biyu da kotun musamman ta kasar Iraki ta bayar da faifai game da tambayar Sadam da muhimman mabiyansa tambayoyi,wannan ya nuna mana cewa,za a yanke wa Sadam hukunci.Amma da sauki ne ake iya ganin cewa,tun bayan da aka kama Sadam a cikin watanni 18 da suka shige,aikin yanke masa hukunci yana cikin mawuyacin hali.
1 2 3
|