A cikin `yan kwanakin da suka shige,halin da kasar Iraki ke ciki bai sami kyautatuwa ba.Tun bayan da aka kafa gwamnatin wucin gadi ta kasar Iraki a ran 28 ga watan Aflilu na wannan shekara,gaba daya yawan mutanen kasar da suka mutu a cikin hare-haren da aka kai musu ya riga ya kai kusan dari 9.Daga watan Maris na shekara ta 2003 wato bayan barkewar yakin Iraki,yawan sojojin kasar Amurka da suka mutu a kasar Iraki ya riga ya zarce dubu daya da dari bakwai.Gwamnatin kasar Iraki tana fatan za a kai bugu ga mabiyan Sadam da masu tsattsauran ra`ayi na rukunin Sunni ta hanyar yanke wa Sadam hukunci,saboda suna yin ayyukan nuna karfin tuwo don nuna kiyayya ga kasar Amurka da kuma nuna kiyayya ga gwamnatin kasar Iraki.Kafin makonni biyu da suka shige,makiyin Sadam kuma shugaban gwamnatin wucin gadi ta Iraki ta yanzu kuma shugaban kurdawa Jalal Talabani ya gaskanta cewa,Sadam zai fito a kotu cikin watanni biyu masu zuwa.Kakakin gwamnatin wucin gadi Laith Kuba ya bayyana a ran 5 ga wata cewa,gwamnatin Iraki tana so ta yi hanzari ta yanke wa Sadam hukunci.Firayin minstan kasar Ibrahim al-Jaafari ya yi habaicin cewa,idan an yanke wa Sadam hukuncin babban laifi,wata kila za a yanke masa hukuncin kisa.
Amma a ran 7 ga wata,kotun musamman mai kula da aikin yanke wa Sadam hukunci ta bayar da wata sanarwa cewa,ya zuwa yanzu ba a tanadi hakikanin lokacin yanke wa Sadam hukunci ba.A sa`i daya kuma,wani kakakin kotun musamman ya musunta wannan.A wannan rana kuma kakakin firayin ministan kasar Iraki ya amince da cewa,kotun musamman za ta tsai da dukkan kudarai game da Sadam.
1 2 3
|