
A kan hauhawar kara kai farmaki da ake yi, sabuwar gwamnatin kasar Iraq da sojojin kasar Amurka dake kasar Iraq sun dauki wadansu matakai, ciki har da daga ran 7 zuwa ran l4 ga watan nan da muke ciki, an yi fama mai tsanani ga 'yan ta'addanci dake iyakar kasa ta tsakanin kasar Syria da kasar Iraq. A ran l4 ga watan nan da muke ciki, rundunar soja ta kasar Amurka dake Iraq ta bayar da wata sanarwa cewa, a cikin farmakin da aka yi, a klla dai an kashe 'yan ta'adda l25, kuma yawan mutanen da aka kama sun kai 39, har an yi ganimar makamai da kayayyakin soja da yawa sosai. Bugu da kari kuma, sojoji 9 na kasar Amurka sun mutu, kuma mutane 40 sun ji rauni.
Amma, sojojin kasar Amurka da sabuwar gwamnatin kasar Iraq ba su sassauta tsanantaccen halin da ake ciki a kasar Iraq ba. Cikin 'yan kwanakin da suka shige, al'amuran fashewar boma bomai da kai farmaki sun yi ta faruwa bi da bi. Kuma a ranar da malama Rice ta isa kasar Iraq, kuma a wurare daban daban na kasar Iraq, an yi ta fashewar boma bomai da kai farmaki har sau da yawa, kuma mutane a kalla dai 8 sun mutu, kuma mutane gomai da suka ji rauni.
An ce, a cikin tsanantaccen halin da ake ciki ne ba zato ba tsammani,malama Rice ta kai ziyara a kasar Iraq wannan ya bayyana cewa, kasar Amurka tana goyon bayan sabuwar gwamnatin kasar Iraq, Kana kuma don tattaunawa tare da sabuwar gwamnatin kasar Iraq kan yadda ake yin gaba da tsanantaccen halin da ake ciki a kasar Iraq, da kara karfin sake gina kasar Iraq da tsara sabon tsarin mulkin kasar Iraq.
1 2 3
|