
Domin sake maido da kwanciyar hankali da zama mai dorewa, da tabbatar da ajandar sake kafa mulkin Iraq lami lafiya, bayan kafuwar sabuwar gwamnati ta Ibrahim al-Jaafari ta tafiyar da matakai tare da sojojin Amurka, ga kungiyoyin dakaru na Iraq. A sa'an nan kuma Jaafari ya nada mutanen Sunni 4 da su zama 'yan majalisar ministoci, ciki har ministan tsaro, yana fata ta tasirinsu na siyasa da kwarjininsu cikin kabilar, zai yi cudanya da dakaru na Sunni har kai ga shawo kansu da su yar da nuna karfin tuwo da kai farmaki. Amma duk kokarin ba su sauya halin kwanciyar hankali na Iraq ba.
Na biyu, wadannan kungiyoyin dakaru ba su amince da matsayin halal na sabuwar gwamnatin Iraq da aka kafa cikin mamayewar sojojin Amurka ba. Daga wadannan waje kuma, sabane-sabane na kabilu da na addinai sun yamutse da ke tsakanin darikar Shi'a da musulmi kuma tsakanin kurdawa wadanda kuma ke da daddaden lokaci, wannan shi ne wani babban dalilin da ya sa, da kyar gwamnatin Iraq ta zaunad da halin kwanciyar hankali. Saboda sabane-sabane sun yamutse, ta yaya za a kai Iraq da ta fita daga wajen karfin tuwo, akwai nauyi da yawa kuma hanyar samun nasara tana da nisa a gaban gwamnatin Jaafari.(ASB) 1 2 3
|