
Ran 11 ga wata ya zama ranar zuba da jini cikin kasar Iraq. Bisa labarin da tashar TV ta Al-jazeera ta bayar da cewa, a wannan rana, fashewa da kai farmaki ga sojojin Amurka da ke jibge cikin Iraq da 'yan sanda na Iraq da sojojin da suka yi rajista don shiga cikin 'yan sanda, a kalla dai mutane 78 sun mutu, kuma mutane wajen 150 sun sami rauni. Ranar ta zama ranar da aka sa mutane mafiya yawa da sun mutu ko sami rauni tun bayan kafuwar sabuwar gwamnatin Iraq.
Kafofin watsa labaru na Larabawa sun nuna a ganinsu cewa, fashewa da kai farmaki sun yi ta aukuwa 'yan kwnaki cikin Iraq, wanda ke jibintar da sojojin Amurka da ke jibge cikin Iraq su yi aikin danne dakaru masu yin adawa da Amurka a shiyyar Qaim da ke arewa maso yamma na Iraq wato lardin Anbar ke kusad da iyakar kasar Syria. Domin yin ramma gayya da nukura ga aikace-aikacen sojojin Amurka, dakaru na Iraq sun tada wani sabon tashe wajen fashewa da kai farmaki.
1 2 3
|