Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-05-12 17:28:15    
Me ya sa an yi ta nuna karfin tuwo cikin kasar Iraq

cri
 

Ran 7 ga wata da dare a shiyyar iyakar kasar Iraq sojojin Amurka sun soma aikace-aikacen danne mai suna Matador wanda ke mai da mashin gaba kan Abu Musab Al-zarqawi, madugun kungiyar al-qaeda da sauran mabiyansa,'yan dakaru na kasashen waje da ke boya cikin shiyyar. Wannan dai ya zama manyan aikace-aikacen soja tun bayan sojojin Amurka sun kai farmaki ga Faloujah babban sansanin yin adawa da Amurka da aka yi a watan Nuwanba na bara. Cikin 'yan kwanaki, sojojin Amurka da 'yan dakaru sun yi dauki ba dadi a lardin Anbar, kuma sojojin Amurka sun kewaye shiyyar Qaim. Sojojin Amurka sun gaskanta cewa, a kalla dai 'yan dakaru masu yin adawa da sojojin Amurka dari sun mutu, gefen sojojin Amurka kuwa sojoji 14 sun mutu cikin aikace-aikacen danne, haka ya sa adadin matattu sojojin Amurka na tun bayan barkewar yakin Iraq ya zarce mutane 1600.

Manazarta al'amuran yau da kullum sun nuna cewa, aikace-aikacen danne mai suna Matador da sojojin Amurka sun yi ya zama wani dalili na kusa-kusa da ke haifar da halin zama da Iraq ke ciki bai sami sassautawa ba , maimakon haka halin ya sake fado cikin karfin tuwo, ba kamar yadda mutane ke sa rai saboda kafuwar sabuwar gwamnati ba. Babban dalili shi ne har kullum yawancin kungiyoyin dakaru na Iraq ke tsaya kan yin adawa da mamayen sojojin Amurka.


1  2  3