Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-04-15 13:27:30    
Halin da ake ciki a kasar Iraki

cri

A baya ga haka kuma, daya daga cikin manyan batutuwan da Mista Zoellick da shugabannin kasar Iraki suka yi tattaunawa a kai shi ne sake gina kasa cikin kwanciyar hankali. Kasar Amurka tana fata sabuwar gwamnatin kasar Iraki za ta kara daukan matakai domin kai naushi ga dakarun da ba sa ga maciji da kasar Amurka. Bayan da Jalal Talabani ya zama shugaban kasar Iraki, ya riga ya dauki matakai da yawa domin yaki da dakaru masu adawa da kasar Amurka. A fanni daya, ya nuna cewa, zai yafa wa wadanda suka fito daga dakarun laifi. A dayan fanni kuma, sojojin kasar Iraki da na kasar Amurka suna ta kokarin kama wadanda ake zarginsu da shiga dakarun 'yan hamayya. Wannan ya sa dakarun 'yan hamyya suka ji fushi sosai, sun dau niyyar ci gaba da kai jihadi ga sojojin Amurka da 'yan sandan Iraki. Dakarun da Abu Musab al-Zarqawi, shugaba na uku na kugiyar Al-Qaedam ke shugabantar sun yi kurarin cewa, an yi fashewar bomabomai a gaban ginin ma'aikatar harkokin gida a ran 14 ga wata ne, domin nuna wa kasar Amurka cewa, ba za a iya rushe dakaru masu adawa da kasar Amurka ba.

Manazarta suna ganin cewa, yanzu jama'ar kasar Iraki suna so su samu kwanciyar hankali da zaman lafiya, shi ya sa idan sabuwar gwamnati ta dauki mataki mai amfani, za a kwantar da kurar da ta tashi. Amma, matukar sojojin kasar Amurka ba su janye jikunansu daga kasar Iraki ba, to, babu makawa, ba za a daina farmaki ga sojojin Amurka da masu goyon bayan kasar Amurka ba. (Bello)


1  2  3