
A kwanan baya ba da jimawa ba, Donald Rumsfeld, ministan tsaron kasar Amurka da Robert Zoellick, mataimakin sakataren harkokin waje na kasar Amurka, sun kai ziyara ga kasar Iraki. A ran 12 ga wata, Mista Rumsfeld ya kalubalanci sabbin shugabannin kasar Iraki da su kafa majalisar ministoci tun da wuri. A ran 13 ga wata kuma, Mista Zoellick ya yi tattaunawa da sabbin shugabannin kasar Iraki kan aikin sabuwar gwamnati wajen siyasa da tattalin arziki da tsaron kasa. Manazarta na ganin cewa, al'amuran zub da jini da aka yi a kasar Iraki a kwanakin baya suna da nasaba da ziyarar Mista Rumsfeld da Mista Zoellick a kasar.
Da farko, a lokacin ziyararsa, Mista Rumsfeld ya yi nuni da cewa, kasar Amurka ba ta da shirin janye sojojinta. Shi ya sa dakaru masu adawa da kasar Amurka suna ta kai farmaki domin neman kore sojojin kasar Amurka daga kasar Iraki.
Ban da wannan kuma, ziyarar da Mista Rumsfeld ya kai wa kasar Iraki ta nuna mana cewa, kasar Amurka tana so ta kafa wata gwamnatin dimokuradiyya a kasar Iraki, ta yadda za ta zama abin koyi ga sauran kasashen gabas ta tsakiya. Shi ya sa dakarun kasar Iraki suna ta da tarzowa, domin kai naushi ga kasar Amurka kan yunkurinta na sayar da mulkin dimokuradiyya irin na Amurka a duk duniya.
1 2 3
|