
Ran 14 ga wata, an sake zub da jini da yawa a kasar Iraki. Gidan telebijin na Al-Jazeera ya bayar da labarin cewa, a ran nan, an yi fashewar bom a cikin mota har sau biyu a gaban babban ginin ma'aikatar harkokin gida ta kasar da ke kudancin birnin Bagadaza, inda aka haddasa mutuwar mutane a kalla 18, da kuma ji wa wasu 40 rauni. Kuma a cikin mutanen da suka mutu ko jikkata, yawancinsu 'yan sanda ne. Ban da wannan kuma, an kai hare-haren bomabomai a wuraren dabam daban na kasar Iraki a ran nan. Wannan ya sa mutane a kalla 70 suka rasa rayukansu ko kuma ji rauni.
Kafin wannan kuma, a ran 13 ga wata, an yi fashewar bomabomai a wasu biranen kasar Iraki, inda aka kashe mutane 9 da kuma ji wa wasu 15 rauni, kuma yawancinsu 'yan sanda ne na kasar Iraki. A dai dai wannan ra na kuma, an kashe wani sojin kasar Amurka a garin Ramadi da ke yammacin kasar Iraki.
1 2 3
|