
Sabo da ba a kafa sabuwar gwamnatin wucin gadi a lokacin da aka kayade ba, al'amuran kunar bakin wake sun yi ta wakana a wurare daban daban na kasar Iraq, har kowace rana mutane sama da goma suna jin rauni, cikin masu shan wahala yawancinsu farar hula ne. Mummunan muhallin kwanciyar hankali ya haddasa ajandar sake raya tattalin arzikin Iraq ba ta sami ci gaba ba, 'yan kasa ba su sami kyautatuwar zaman rayuwa ba.
Manazarta sun nuna cewa, ya kamata bangarori daban daban na Iraq su bi niyyar jama'a, su yi sauri don kiran taro na biyu na majalisar wucin gadi, cikin taron za a ci gaba da yin shawarwari kan batun kafa sabuwar gwamnati. Sai dai ta haka ne kawai jama'ar Iraq za su maido da imaninsu kan sake raya kasa, kuma za su sake shiga cikin ayyukan raya makomarsu.(ASB) 1 2 3
|