
Yanzu sabanin da ke kasancewa tsakanin bangarorin shi ne, jam'iyyar kawancen hadin kai ta Iraq da kungiyar kishin kasa ta Kurdawa suna neman samun muhimmin mukami na ministan man fetur. Kuma suna fata za a ba ministan tsaron kasa, mukamin aiki mai wuya, mai kula da kai naushi kan dakaru yin adawa da Amurka na darikar Sunni ga 'yan darikar Sunni, amma da'rikar Sunni ba sua ba da amsa da gaske ba.
Kafofin yada labarai na Larabawa sun nuna cewa, a ran 30 ga watan Janairu wato bayan kammala babban zabe na kasar Iraq, bangarori daban daban sun yi shawarwari kan batun kafa majalisar, cikin shawarwarin da aka yi har cikin tsawon watanni biyu, koda yake bangarorin sun sami ra'ayi daya kan wasu batutuwa, amma a kan batutuwan da ke shefar moriyarsu, suna rike da ra'ayinsu, haka ya haddasa taro na farko na majalisar wucin gadi ya bi ruwa.
1 2 3
|