Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-03-28 17:39:39    
Za a kammala shawarwarin kafa majalisar minisstoci na bangarorin kasar Iraq

cri

Ba a yi taro na biyu na majalisar ministoci ta wucin gadi ta Iraq kafin ran 27 ga wata kamar yadda aka kayadde ba, amma Ibrahim al-Jaafari mai dan takaran zama firayim minista na jam'iyyar kawancen hadin kai ta Iraq wato da'irar shi'a, kawancen babbar jam'iyyar siyasa ta farko ta majalisar wucin gadi, ya nuna cewa, an yi kusan kammla shawarwarin kafa majalisar ministoci, ana sa ran cewa cikin kwanaki masu zuwa za a sanar da kafa sabuwar gwamnati. Barham Saleh mataimakin firayim ministan gwamnatin wucin gadi ta Iraq kuma daya daga cikin shugabanni na rukunin Kurdawa ya nuna wadatar zuci wajen yin hasashe cewa, kafin ran 29 ga wata bangarori daban daban za su sami ra'ayi daya kan batun kafa majalisar.

Wakilai masu halartar shawarwarin kafa majalisar na jam'iyyar kawancen hadin kai ta Iraq da na kungiyar kishin kasa ta Kurdawa, bangarorin biyu sun sami ra'ayi daya kan batun rarraba yawancin mukamai : wani shugaba Musulmi na darikar Sunni zai zama shugaban majalisar wucin gadi, kila shugaba Ghazi al-Yawar na gwamnatin wucin gadi ne kuma mataimakan shugabannin majalisar biyu za su fito daga 'yan darikar Shi'a da darikar Sunni ; Jalal Talabani shugaban kungiyar kishin kasa ta Kurdawa zai zama shugaban kasa, mataimakansa biyu za a gabatar da sunayensu daga cikin 'yan darikar Shi'a da darikar Sunni : Ibrahim al-Jaafari da jam'iyyar kawancen hadin kai ta da'irar Shi'a ta gabatar da sunansa zai zama firayim minista.

1  2  3