
Na uku, batun janyewar sojoji zai kawo martani daya bayan daya. Rundunonin sojojin kasashen waje da ke girke a kasar Iraki sun sake mai da hankulansu ga janyewar jiki daga kasar Iraki, wannan ba ma kawai zai kawo tasiri ga manyan kasashen da suke tura sojoji zuwa Iraki ba, hatta ma ga kasar Amurka da kasar Britaniya da Australiya wajen aiwatar da shirin shimfida sojojinsu, sa'anan kuma zai kawo babban matsin lamba ga kasar Poland da sauran kasashe. In lokacin ya yi, to rundunar sojojin kasashen waje da ke ci gaba da kasancewa a cikin kasar Iraki za su fuskanci matsalar rashin wadanda za su maye gurabun sojojin kawancensu bayan da suka janye jikinsu daga kasar Iraki . Alal misali, a tsakiyar watan Maris na shekarar da muke ciki, sojojin kasar Hungari za su janye jikinsu daga kasar Iraki.
Manazatan al'amarin nan sun bayyana cewa, ma'anar siyasa da aka samu wajen janyewar sojojin kasashen kawancen kasar Amurka da Britaniya ta fi ma'anar sha'anin soja. An bayyana cewa, lokaci bai yi ba da rundunar sojojin tsaron kai ta kasar Iraki za ta iya daukar nauyin tsaron kai, saboda haka dole ne sojojin kasar Amurka da Britaniya su kara tura sojojinsu da yawa zuwa kasar Iraki. lallai wannan zai kara sanya sojojin Amurka da Britaniya su shiga halin kebancewa .(Halima) 1 2 3
|