
Wakilin Rediyo kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa, a ranar cika shekaru biyu da aka tayar da yakin Iraki, wasu kasashen da suka hada da Italiya da Bulgaria da Ukraine da Portugal da sauransu wadanda suka nuna goyon baya ga kasar Amurka wajen tayar da yaki a kasar Iraki da kuma girke sojoji a kasar bi da bi ne suka gabatar da burinsu na janye sojojinsu daga kasar Iraki. Bisa wannan halin , a ran 16 ga wannan wata a birnin Washington, shugaban kasar Amurka W.Bush ya kira taron ganawa da manema labaru, inda ya bayyana cewa, ya fahimci wadannan kasashe da suke da burin janye sojojinsu daga kasar Iraki, amma bai kamata ba su janye sojojinsu daga kasar, sai zuwa lokacin da 'yan sanda da runduanr sojojin tsaron kai na kasar Iraki suke iya daukar nauyn aikinsu bayan janyewar sojojin taron dagi, Manazartan al'amarin suna ganin cewa, idan kasar Amurka tana son shawo kan sauran mambobin da ke cikin rundunar sojojin taron dangi da su ci gaba da tsugunar da sojojinsu a kasar Iraki, to mai yiyuwa ne wannan zai zama mawuyacin aiki gare ta. Akwai manyan dalilai guda uku:
1 2 3
|