
Na farko, ba a san yaushe ne za a cim ma burin shimfida zaman lafiya a kasar Iraki ba. Harkokin siyasa da ake gudanarwa a kasar Iraki wadda kasar Amurka ta sa hannu a cikin aikin tsara fasalinta na tafiya sannu sannu. Wadanda suke cikin kawancen Amurka suna kara fahimta cewa, Iraki da ke kasancewa bayan yaki ba ta yi kama da bayanin da shugaba Bush ya yi ba, wato ta riga ta shiga cikin sabon zamani da ke da dimokuradiya da zaman walawa da wadatuwa. Bayan da aka kawo karshen babban yakin a kasar Iraki har zuwa yanzu, jama'ar Iraki ba su sami tabbacin da aka musu alkawari wajen zaman rayuwa ba, kuma ba a kawo musu babban sauyi wajen samar da abinci da magungunan sha da aikin likitanci da karfin lantarki da ruwan sha ba, sojojin taron dangi da gwamnatin Iraki suna ta kara zama takitin da masu goyon bayan tsohuwar gwamnatin Iraki da dakaru iri iri suke kai musu farmaki, kuma aikace-aikacen nuna karfin tuwo da na ta'addanci suna ta bullowa ba tare da fashi ba, sabanin da ke tsakanin al'umma da addinai a zamantakewar al'umma yana kara tsananta.
Na biyu, Halin da kasar Iraki ke ciki na tsaron kai da ke kara tsananta ya sanya gwamnatocin da sojoji cikin halin matsin lambar matsi wajen siyasa.
1 2 3
|