
Jama'ar kasar Italiya ba su amince da matsayin da gwamnatin take dauka kan yakin Iraki ba. Amma gwamnatin ta tura sojoji dubu 3 zuwa kasar Iraki. Bayan aukuwar matsalar, kodayake firayin minista Berlusconi na kasar Italiya ya jadadda cewa ba za a canja manufar da gwamnatinsa take bi kan kasar Iraki ba, ya kuma ce har yanzu kasar Italiya kasa ce da ke abuta da kasar Amurka. Amma an nuna cewa, wa'adin aikin sojojin Italiya da ke kasar Iraki zai sa aya a karshen watan Yuni na shekarar nan. An kuma riga an fara share gafe don babban zabe na shekarar 2006 a kasar Italiya. Sabili da haka, yanzu gwamnatin Italiya tana fuskantar matsin da ake mata sosai. Sabo da haka, ko za ta iya kwantar da hankalin jama'ar Italiya, wannan wani babban kalubale mai tsanani da gwamnatin Berlusconi ke fuskanta. (Sanusi Chen) 1 2 3
|