 A ran 6 ga wata, 'yar jarida ta kasar Italiya Giuliana Srena ta wallafa wani bayani mai lakabi Hakakanin Gaskiya a kan jaridar Il manifesto inda take aiki. A cikin bayaninta, malama. Sgrena ta zargi sojojin Amurka da cewa sun bude mata wuta da gangan domin bangaren Amurka ya ki yarda da gwamnatin Italiya ta yi shawarwari da masu rike da makai na Iraki don yunkurin neman sakinta. Wannan bayani ya tayar da hankali sosai a kasar Italiya.
A cikin bayaninta, malama Sgrena ta nuna cewa, dalilin da ya sa bangaren Amurka ya yi haka shi ne kome wahala, yana son hana duk kokarin da gwamnatin Italiya ta yi domin kubutar da ita daga hannun masu rike da makamai na Iraki. Bisa labari daban da kafofin Italiya suka bayar, an ce, mai yiyuwa ne gwamnatin Italiya ta biya wa masu rike da makamai kudi mai yawan gaske. Wannan abu ne da bangaren Amurka ba ya son gani. Bangaren Amurka yana ganin cewa, idan an yi haka, to, za a ingiza masu rike da makamai na Iraki da su kara yin garkuwa da mutane. Malama Sgrena ta ce, ba ta san ko gwamnatin Italiya ta biya masu rike da makamai na Iraki kudi mai yawan gaske domin kubutar da ita daga hannunsu ba, amma ba ta yarda da abubuwan da bangaren Amurka ya fadi a cikin wata sanarwar da ya bayar bayan aukuwar matsalar ba. A cikin sanarwar bangaren Amurka, an ce, domin motar da Sgrena ke ciki na gudu da sauri sosai lokacin da take wuce tashar bincike ta sojan Amurka. Sojojin Amurka da ke tashan sun taba ba ta alamar tsayawa, amma ta kyale wannan alama. Sakamakon haka ne sojojin Amurka suka bude wa motar wuta. Amma cikin bayanin da Sgrena ta rubuta, malama Sgrena ta ce, lokacin aukuwar matsalar, motar da take ciki tana gudu cikin saurin kamar yadda aka saba. Kafin a bude wa motar wuta, ba ta ga kowace alama ba.
1 2 3
|