
Bayan jama'ar Italiya sun sami labarin aukuwar matsalar, sun yi bakin ciki kwarai. A ran 6 ga wata, jama'a dubbai sun yi zanga-zanga sun nuna ta'aziyya ga Nicola Calipari wanda aka harbe shi a cikin matsalar. Ban da wannan, mutane daruruwa sun yi zanga-zanga a wajen kokar ofishin jakadancin kasar Amurka da ke kasar Italiya, inda suka nemi gwamnatin Amurka da ta binciki matsalar sosai da sosai tun da wurwuri kuma ta samar da sakamakon binciken. Wasu mutanen da ke yin zanga-zanga sun kuma nemi kasar Amurka da sauran kasashe wadanda suka tura sojojinsu a kasar Iraki da su janye jikin sojojinsu daga kasar Iraki.
A sa'i daya, kafofin kasar Italiya sun mai da hankali sosai kan wannan matsala, inda da kakkausar harshe ne suka nemi gwamnatin Berlusconi da ta matsa wa kasar Amurka lamba domin neman gaskiyar matsalar. Wasu jaridu sun kuma yi sharhi cewa, muhimmin dalilin da ya sa aka haddasa wannan matsala shi ne an yi yakin Iraki ba bisa adalci ba.
Yanzu, hukumar bincike ta Rome ta riga ta shirya binciken wannan matsalar sosai da sosai. Ma'aikatar shari'a ta kasar Italiya ta ba da umurni umurni, inda ta nemi hukumar 'yan sanda ta tambayi wadanda suka ga aukuwar matsalar domin neman shaidu.
1 2 3
|